Skip to content Skip to footer

Auren Kwangila by Sumayyah Abdulkadir

1,400.00

Box contains: Book 1, 2, 3 and 4

 

Also from the Author

Category: Product ID: 3153

Description

A tunanin sa in har zai samu MU’AZATU he can manage any situation ….. Ciki kuwa har da fushin mahaifiyar sa….. Sai al’amarin ya zo alal akasi ga tunanin sa; in managing everything got mismanaged tunda kuwa batan basira da sabawa iyaye a sirrance ya shigo ciki. Batan basirar da ta kai shi yin KWANGILA a cikin aure don cimma son zuciya. Dalilin sa na yin hakan shine; ya gwada shawarwari ukun da zuciyar sa ta kawo don gujewa auren SUHAANAHr da basu san asalin ta ba….. Duka shawarwari biyun farko basu bada hanya mai bullewa a gareshi ba, basu kawo mafitar da zai tsira daga auren SUHAANAH ba. Mafitar na ga ta ukun, amma cike take da wauta da toshewar basira hadi da karkacewa daga umarnin Ubangiji. Wannan mafitar guda daya ce; maida auren da mahaifiyar sa k son sa da shi zuwa na KWANGILA don tsira da Mu’azatu! Wannan yarjejeniya ta kasance a tsakanin su su biyu ba da sanin mahaifiyar sa ba, wadda a tunanin sa dukkan su za su amfana da ita, kowannen su ya kai ga cikar burin sa. To amma shin soyayya na karbar yarjejeniya ne daga dan adam ta yi la’akari da ita a lokacin da za ta nemawa kanta muhalli? Wannan wani al’amari ne wanda daga shi har HAFSAT-SUHAANAH ba su da masaniya a kai. Abinda ya biyo baya mai tsauri da girma ne da ya shallake tunanin su. In his effort to escape daga auren Suhaanah don samo Mu’azatu lokaci bai bashi dama ba, zuciya ta yi halin dawurwura irin nata, komai ya damalmale masa yadda ba zai iya gyarawa ba!!

– Takori

Additional information

Part

1, 2, 3, 4

Reviews

There are no reviews yet.

Be the first to review “Auren Kwangila by Sumayyah Abdulkadir”

Your email address will not be published. Required fields are marked *